1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun dukufa yaki da Coronavirus

Gazali Abdou Tasawa
January 30, 2020

Tun dai bayan bullar cutar Coronavirus a Chaina in da tahalaka mutane da dama da ma yaduwarta a wasu kasashe, kasashen duniya suka dukufa daukar matakan rigakafin yaduwar cutar a kasashensu

https://p.dw.com/p/3X2T2
China Coronavirus Queen Elizabeth Hospital in Honkong
Hoto: Reuters

Tun dai bayan billar cutar Coronavirus a kasar Chaina inda ta halaka mutane da dama, da kuma yaduwarta a wasu kasashen, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da sauran kasashen duniya suka dukufa wajen daukar matakan rigakafin yaduwar cutar a cikin kasashensu. A yayin da wasu kasashen suka tsaurara matakan gudanar da bincike a filayen jiragen sama da na kasa da ma na ruwa na kasashensu, musamman na fasinjan da ke fitowa daga kasar Chaina, wasu kasashen irin su Amirka da Faransa da Japan sun dauki matakin kwaso mutanensu daga kasar ta Chaina zuwa gida.