1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Corona ta bulla a wasu kasashe

Zainab Mohammed Abubakar
January 25, 2020

Shugaba Xi Jinping na China ya bayyana bukatar daukar matakan gaggawa dangane da babban kalubale da kasarsa ke fuskanta na barkewar annobar cutar Corona da ke cigaba da yaduwa tsakanin jama'a.

https://p.dw.com/p/3Wnc6
China Coronavirus Queen Elizabeth Hospital in Honkong
Hoto: Reuters

Sama da mutane dubu daya ne hukumomin lafiyar kasar ta China suka tabbatar da cewar, sun kamu da wannan cuta da a yanzu haka ke kara bazuwa zuwa kasashen da ke yankin Asiya da ma kuma Turai, ciki har da Faransa.

Cutar Corona dai ta yi wa duniya dirar mikiya, da a yanzu haka ya tilasta kwararru a fannin kula da lafiya da likitoci daukar mataki na gano yadda za a shawo kanta. 

A cewar shugaba Jinping dai, rai nada matukar muhimmanci. Dalili kenan da ya sa ake daukar matakan gaggawa da zarar an samu barkewar annoba, tare da daukar matakan shawo kanta, kamar yadda masani kan cututtuka masu yaduwa a birnin London Dr Adam Kucharski ya yi karin haske: 

Der chinesische Präsident Xi Jinping besucht Griechenland
Shugaba Xi Jinping na ChinaHoto: AFP/A. Messinis

"A gaskiya a kowace rana muna kara ilimantuwa, kasancewar har yanzu ana lalube ne cikin duhu dangane muhimman abubuwan da ya dace a sani kan yadda wannan cuta take yaduwa. Kwayoyin cutar na bukatar akalla kwanaki 3-6 a jikin mutum, hakan ne zai kawo jinkiri wajen bayyanar alamunsa. Alal misali idan mutum na dauke da kwayoyin cutar kuma yana balaguro, zai dauke shi mako guda kafin alamomi su fara bayyana, kuma lokacin ne za a iya sani".

Masu fada aji na gwamnatin Chinar dai sun gudanar taro a jiya Asabar, biyo bayan umurnin majalisar mulkin kasar kan bukatar girka na'urorin nazarin yanayin jikin bil'adama a dukkan filayen jiragen sama da na kasa. Kama da wannan rana ta Lahadi a haranta zirga zirgar bas bas na Fasinja shiga ko kuma fita da birnin dake zama fadar gwamnati

Lei Haichao, shi ne darectan hukumar kula da lafiya a birnin Beijing:

"Hukumomin birane da gundumomi sun kafa tawagar jami'an da zasu dauki nauyin kulawa da lamarin. An kuma zabi manyan asibitotoci guda uku da zasu taimaka. Ana bada horo na musamman daura da daukar matakan jinya. Muna amfani da tsarin kula da lafiya na Chinese a gargajiyance da kuma na bature. Mun kebe cibiyoyin kula da guda 101, da sashin kula da zazzabi mai tsanani, tare da baiwa marasa lafiya da ke da fama da zazzabi shawarwari".

Deutschland Forschung Coronavirus
Cibiyar binciken cutar Corona na JamusHoto: picture-alliance/dpa/C. Gateau

A yanzu haka dai gwamnati kasar China ta kara zuba kudi a Wuhan, da karin jami'an kiwon lafiya 1,200 da ke cikin shirin kota kwana a wannan karshen makon, wanda ke zuwa daidai lokacin da hukumar lafiyar kasar ta sanar da mutuwar mutane sama da 40 biyo bayan kamuwa da annobar cutar Corona.

Ya zuwa yanzu dai kasashen da cutar ta bulla sun hada da Malasiya da Japan da Koriya ta Kudu sai Taiwan da Thailand da Vietnam da Saudi Arabia da Singapore da Amurka da Australiya da Macau dake karkashin ikon China. 

Kwamissionar lafiya ta Tarayyar Turai Stella Kyriakides ta kira taron wakilan hukumomin lafiya na EU a gobe Litinin domin tattauna matakai kan cutar, bayan bullarsa a kasar Faransa. ))