Erdogan na ziyara a Jamus
September 28, 2018Talla
Shugaba Racep Tayip Erdogan na kasar Turkiyya ya isa kasar Jamus a wata ziyarar aiki da ake ganin kokari ne na sasanta rigimar kasar da Jamus da ta tsananta cikin shekaru biyun da suka gabata.
Gabanin tashinsa daga Turkiyyar dai Shugaba Erdogan wanda a baya ya zargi Jamus da akidar 'yan Nazi, ya bayyana karara cewa kasarsa na da bukatar dinke baraka da Jamus.
Daga cikin matsalolin da kasashen biyu ke rigima kansu dai sun hada da tsare wasu Jamusawa bakwai da Turkiyya ke yi, da kuma Jamus ta ce lallai ne a sake su kafin su kai ga sasantawa.
Jamus dai ta karrama shugaban na Turkiyya, sai dai ziyarar ta kai ga rufe wasu muhimman sassa na birnin Berlinfadar gwamnatin kasar, saboda yadda wasu ke adawa da ziyarar ta Shugaba Erdogan.