1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS: Sojojin Nijar su mika mulki cikin wata tara

August 31, 2023

Shugaban Najeriya kana shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu ya shawarci gwamnatin mulkin soji a Nijar da ta mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da wata tara.

https://p.dw.com/p/4Voyk
Nigeria Abuja | ECOWAS Gipfel
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Shugaban ECOWAS ko CEDEAO, Bola Ahmed Tinubu ya shawarci gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soji a Nijar da ta mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da wata tara kamar yadda aka gani a Najeriya a lokacin da ta fuskanci juyin mulki a shekarun 1990. Shugaba Tinubu ya ce, a shekarar 1999 aka samu nasarar mayar da Najeriya kan tafarkin dimokradiyya bayan kafa kwamittin mika mulki cikin wata tara a zamanin mulkin Janar AbdulSalami Abubakar, wanda ke daga cikin tawagar shiga tsakani domin sasanta dambarwar siyasar Nijar din.

Karin bayani: ECOWAS: Sasanta rikici da sojojin Nijar

A cikin sanarwar da ya fitar, shugaba Tinubu ya ce bai ga dalilin da zai sanya sojojin Nijar su gaza kwaiwayon Najeriya idan har sun yi juyin mulkin ne domin sake yi wa kasar kyakyawan seti.

Shugaban ya kuma kara da cewa, kungiyar ECOWAS ba za ta sassauta takunkuman da ta kakabawa Nijar din ba har sai kasar ta koma kan tafarkin dimokradiyya.

Karin bayani: Ecowas za ta yaki sojojin Nijar