1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Nijar na cikin zaman dar--dar

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
August 11, 2023

Jaridun Jamus sun mayar da hankali a kan takun saka da ake yi tsakanin Ecowas da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da halin da ake ciki a Sudan da kuma matsalar yunwa da al'umma ke fama da ita a Habasha.

https://p.dw.com/p/4V35K
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Jaridar ZEIT ONLINE a sharhinta mai taken: Matsin lambar da bai cimma nasara ba, Najeriya na ganin matakin diflomasiyya ne mafita ga juyin mulkin Nijar. Jaridar ta ce: Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta yi barazanar daukar matakin sojI a kansu. Sai dai duk da haka shugaban Najeriya  Bola Ahmed Tinubu da ke zaman shugaban kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, na fatan cimma matsayar daukar hanyar diflomasiyya. Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar ta Nijar dai, sun yi mirsisi tare da kin mika kai bori ya hau ga wa'adin mayar da Nijar din kan turbar kundin tsarin mulki da ECOWAS ko CEDEAO din ta ba su. Juyin mukin da sojojin suka yi wa Mohamed Bazoum na Nijar karkashin jagorancin Abdourahmane Tchiani dai, na zaman na baya-bayan nan da yankin Sahel mai fama da barazanar 'yan ta'adda ya fuskanta.

Sudan babu wadataccen wurin da za a ajiye gawarwakin mutanen da suka hallaka

Sudan TRansportt eines menschen auf einer Krankenliege
Hoto: AFP

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta nata sharhin mai taken: Ba wanda ke binne wadanda suka mutu a Khartuom, ba za a iya adana gawarwakin mutane da dama da suka halaka a yakin Sudan ba a babban birnin kasar. Jaridar ta ce rahotannin gawarwaki warwatse a kan hanyoyin a babban birnin kasar Sudan din, sun nuna yadda yakin na watanni hudu ke kara kazanta. Wuraren ajiye gawarwaki a birnin sun cika makil, baya ga yawan daukewar hasken wutar lantarki. Babu wadataccen wurin da za a ajiye gawarwakin mutanen da suka halaka, yayin rikicin sojojin gwamnati da mayakan RSF da ya barke tun a tsakiyar watan Afrilun wannan shekara ta 2023 da muke ciki. Yawan daukewar hasken wutar lantarki da kuma tsananin zafi da hare-haren da ake kai wa cibiyoyin kiwon lafiya, ya sanya fargaba kan yadda za a kula da gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu yadda ya kamata. Tuni dai likitoci ke bayyana fargabar karuwar barkewar cututtuka, kasancewar baya ga matsalar wajen ajiye gawarwakin akwai kuma ta karancin magunguna.

Ana fama da yunwa a Habasha amma kuma MDD ta daina kai dauki

Symbolbild I Hunger in der Welt noch groß
Hoto: Mohammed Mohammed/dpa/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta sharhinta mai taken: Abinci da kalubalen sauyi. Mutane na fama da yunwa a Habasha, amma Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da kai daukin abinci. Kayan agaji na yin batan dabo, tilas gwamnati ta samar da hanyoyin raba kayan agajin cikin gaskiya domin kowa ya samu. Jaridar ta ce: Kasar na fama da dimbin talauci, kuma ba a jima ba da yankin Tigray na Habashan ya sha fama da yakin basasa da ya kara jefa al'umma cikin halin tasku da tsananin yunwa. Tsawon watanni ke nan da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya dakatar da kai agaji Habashan. Koda a shekarar da ta gabata mutane sama da miliyan 160 ne suka samu tallafi, daga babbar hukumar agajin ta duniya a kasashe kimanin 120 na duniya. Sai dai a Habasha ta yi gwaji ne kawai na agajin abinci da kalubalen gyara, inda take son tabbatar da ganin agajin ya kai ga dukkan wanda ke tsananin bukatarsa. A yankunan Habashan da dama dai, an hango ana cinikin kayan agajin a kasuwanni.