Dangantakar Isra'ila da Gaza na muni
April 2, 2018Yawan wadanda suka mutu a rikicin iyakar Gaza da Isra'ila na ranar Juma'ar da ta gabata, ya kai mutum 17 a wannan Litinin a dai-dai kuma lokacin da Falasdinawa ke jan damarar zanga-zanga mai karfi. Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai sun yi kiran a gudanar da cikakken bincike kan rikicin, binciken da mahukuntan Isra'ila suka nuna ja a kai.
Daruruwan Falasdinawa ne suka ji rauni a artabu tsakaninsu da sojojin Isra'ila, rikicin da aka dauki shekaru ba a ga irinsa ba tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Ma'aikatar lafiyar a yankin Falasdinawa ta tabbatar da mutuwar wani matashi Bafalasdinu guda a wannan Litinin, sakamakon raunin da ya ji a rikicin.
Kungiyar Hamas ta yi kiran ci gaba da zanga-zangar da ya kai sojin Isra'ila afka masu a ranar Juma'ar da ta gabata.