1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasar Najeriya

July 12, 2018

Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun soma hadewa don kara wa kansu tagomashi a babban zaben kasar da ake jiran a yi kallo.

https://p.dw.com/p/31Kyt
Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Hoto: DW/U.Haussa

A ci gaba da kokarin neman hanyar karbe goruba daga hannun kuturu, jam’iyyun adawar tarrayar Najeriya sun kulla kawancen da suka kira CUPP da nufin kai karshen mulkin shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Jam’iyyun adawar kasar kusan 40 da suka taru a Abuja sun kuma ce sun kulla kawancen da nufin neman kai karshen mulkin APCn a matakai daban daban cikin kasar. Babban kalubalen da ke gaban masu adawar dai shi ne hadiye buri a kokari na biyan bukata a matakai daban daban na siyasa.

A gefe guda kuwa wata gamayyar mai jam'iyyu 20, ta fito da alwashin ita kuwa za ta mara wa shugabancin na yanzu ne baya don ganin ta ci gaba da ayyukan da ta fara tare da yin gyara a wuraren da ake ganin ba a yi dai dai ba.