1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP27: An gargadi kasashe game da zargin juna

November 18, 2022

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci kasashen da ke taro kan sauyin yanayi na COP27 da su daina yawan zargin juna da suke a kan matsalolin sauyin yanayi da ake ciki.

https://p.dw.com/p/4JisZ
Indonesien | G20 Gipfel in Bali | Treffen Guterres und
Hoto: SNA/IMAGO

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bukaci kasashen da ke taro kan sauyin yanayi a Masar da su daina nuna wa juna yatsa a kan matsalolin duniya na sauyin yanayi.

Wakilan kasashen duniyar dai na sa ran cimma yarjejeniya a taron ne a yau Juma'a, kuma Antonio Guterres ya ce ya lura da rashin yarda da juna tsakanin manyan kasashen da suka ci gaba da kuma masu tasowa.

Guterres ya ce zargin juna da kasashen ke ci gaba da yi a taron, ba makawa zai lalata dangantaka a tsakaninsu.

Su dai kananan kasashen na duniya na neman sai kasashe masu karfin masana'antu sun biya su kudaden da za su ba su damar jure wa radadin matsalolin da sauyin yanayin da suke fama da su, ganin yadda manyan kasashen ke kan gaba wajen fitar da hayakin da ke haddasa wa duniya matsalolin da ake ciki.

Daga nasu bangaren su kuwa kasashen yammacin duniya, sukar matsayin China suke yi a kan tsare-tsaren da suka tsara, kuma ma ba ta sanya kanta cikin kasashe masu biyan diyya.