SiyasaChadi
Chadi: An kashe Yaya Dillo Djérou
March 1, 2024Talla
Gwamnatin Chadin ta musunta zargin kisan na Yaya Dillo Djérou amma magoya bayan jam'iyyar ta 'yan gurguzu ta (PSF), sun ce kisa ne, da aka tsara domin kauda dan takararsu saboda yana zaman barazana ga Mahamat Idris Deby.Sojojin sun kai hari a gidan dan siyasar ne da nufin kamashi saboda zargin da ake yi masa, na yunkurin kashe shugaban kotun kollin kasar, amma suka ce ya ki ya mika wuya, kana ya bude músu wuta kafin daga bisani sun bindigeshi.