SiyasaAfirka
Hari a Chadi ya hallaka mutane da dama
February 28, 2024Talla
Wani hari da aka kai cikin dare kan ofishin hukumar tsaron cikin gida a N'Djamena babban birnin kasar Chadi ya hallaka mutane da dama a cewar gwamnati inda ta zargi wasu mutane a cikin jam'iyyun adawa.
An tura sojoji zuwa kewayen ofishin jam'iyyar adawa ta PSF kamar yadda wani dan jaridar AFP ya ruwaito yayin da aka rufe dukkan hanyoyi da suka dangana da ofishin hukumar tsaron ta cikin gida.
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce harin dai ya zo ne bayan da aka tsare wani jigo na jam'iyyar PSF da ake zargi da yunkurin kashe shugaban kotun kolin kasar ta Chadi