1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIngila

Jagoran diflomasiyya na Burtaniya zai fara ziyara a Afirka

Abdourahamane Hassane
November 3, 2024

Ministan harkokin wajen Burtaniya David Lammy zai fara wani rangadi a wasu kasashen Afirka a ciki har da Najeriya domin kara karfafa hulda da kasashen.

https://p.dw.com/p/4mX6y
David Lammy
David LammyHoto: Mark Schiefelbein/AP Photo/picture alliance

 A matakin farko ministan zai yadda zango a tarrayar Najeriya kafin ya isa a Afirka ta Kudu, inda zai mayar da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, da  neman sabuwar hanya a dangantakar da ke tsakanin London da takwarorinta na Afirka.Wannan ziyara ita ce ta farko da ministan harkokin wajen kasar Burtaniya  zai kai nahiyar, Afirka tun bayan da jam'iyyar  Labour ta dawo kan karagar mulki a farkon watan  Yulin da ya gabata.

.