Burtaniya na fama da yawan fursunoni a gidajen yari
September 6, 2024Gwamnatin Burtaniya, ta ce yawan daurarrun da ke gidajen yari a Ingila da kuma yankin Wales, ya kai wani matsayi na kololuwa, daidai lokacin da ake shirye-shiryen kara yawan adadin fursunonin da za a yi wa afuwa.
Kasar Burtaniya dai ita ce ke kan gaba wajen yawan daure mutane a kafatanin kasashen yammacin nahiyar Turai, inda alkaluma ke nuna cewa tana da mutum 88,521.
Ko a baya-bayan nan ma, wata zanga-zangar kwanaki da aka yi a birnin Southpole bayan kisan wasu 'yan mata 'yan makaranta su uku, ta sanya karuwar wadanda gwamnati tsare akalla mutum dubu da 300.
Tsakanin wannan wata na Satumba da watan gobe ne dai, ake sa ran yi wa daurarru mutum dubu biyar da 500 afuwa, a kokarin ganin an rage cunkoso a gidajen yari Ingila da kuma ma wadanda ke a yankin Wales.