1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Kotu ta haramta wa Bolsonaro damar mulki

July 1, 2023

Tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya nuna rashin jin dadinsa kan haramta masa rike wani mukamin gwamnati na tsawon shekaru takwas da kotun koli ta yi.

https://p.dw.com/p/4TIZI
Hoto: Gustavo Moreno/AP/picture alliance

Hukuncin kotun dai ya nuna cewa tsohon Shugaba Jair Bolsonaro zai kwashe shekaru bakwai daga yanzu kafin ya iya rike wani mukami, wato dai sai shekara ta 2030 saboda shakkun da ya bayyana kan tsarin zaben kasar ta Brazil. Sai dai haramcin bai shafi iyalan tsohon shugaban na Brazil ba, musamman ma matarsa da kuma 'ya'yansa.

Wannan hukunci da kotun ta yanke wa Jair Bolsonaro mai shekaru 68 dai, zai iya shafar makomar siyasarsa musamman damarsa ta sake mulki a Brazil. Mr. Bolsonaro dai ya bayyana hukunci a matsayin cin amana, kuma ya ce zai daukaka kara.