Bolsonaro na fuskantar kalubale a zaben Brazil
October 2, 2022Talla
Bayan wasu makonni na yakin neman zabe mai matukar zafi a Brazil, a wannan Lahadin 'yan kasar sun fita rumfunan zabe inda za su zabi wani sabon shugaban kasa.
Shugaba Jair Bolsonaro da ke rike da madafun gwamnatin a yanzu dai na fuskantar kalubale daga tsohon shugaban kasa, Luiz Inácio Lula da Silva.
Masu hasashe sun ce kuri'un jin ra'ayi jama'a sun nuna alamun tsohon Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva wanda ya mulki Brazil din tsakanin shekarar 2003 zuwa 2010 na iya samun rinjaye a zaben.
Kafin ranar Lahadin ma dai, an jiyo Shugaba Bolsonaro na yanzu na zargin rashin gamsuwa da tsarin zaben da ya ce yana iya yin watsi da sakamakonsa.