Bincike ya tabbatar da mutuwar Prigozhin
August 27, 2023Yayin da yake sanar da sakamakon kwamitin binciken ya tabbatar da cewa sunayen mutane goma da aka gano gawarwakinsu bayan aukuwar hadarin ya zo daidai da jerin fasinjoji da kuma matukan jirgin, ciki kuwa har da Yevgeny Prigozhin, shugaban kamfanin sojojin hayan Rasha na Wagner.
Karin bayani: Putin ya yi ta'aziyar mutuwar Prigozhin
To sai dai kwamitin bai yi ba wani karin bayani kan nau'ikan kwayoyin halittar da ya gudanar da binkicen a kansu ba, sanan kuma bai bayar da haske ba kan ko hadarin na da nasaba da harbi da makami mai linzami ko kuma tashin bam.
Karin bayani: Wagner: Prigozhin ya "mutu" a hadarin jirgi
Daga nata bangare dai gwamnatin Rasha ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi mata na kitsa hadarin ya yi ajalin Prigozhin da mukarrabansa, duba da yunkurin tawayen da yi wa fadar Moscow watanni biyu kafin hadarin.
Karin bayani: Rasha: Kremlin ta musanta kisan Prigozhin