Yevgeny Prigozhin ya "kwanta dama"
August 23, 2023Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Tama ta Rashan ce, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar cewa shugaban rundunar ta Wagner Yevgeny Prigozhin na daga cikin mutane 10 da suka "halaka" a hadarin jirgin saman na 'yan kasuwa. Koda yake tun da fari hukumar ta tabbatar da cewa shugaban na Wagner Prigozhin na cikin jerin fasinjojin da za su hau jirgin, sai dai ba ta yi karin haske kan ko ya hau din ba. Har ya zuwa yanzu dai, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ba shi da tabbacin Prigozhin na cikin jirgi duk da tabbacin "mutuwarsa" da wasu kafafen yada labaran Rashan suka bayar. Kamfanin dillancin labaran Rashan Tass ya ruwaito Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar na cewa, jirgin da wasu rahotanni da ba a tabbatar ba ke cewa mallakin Prigozhin ne na dauke da matuka uku da kuma fasinjoji bakwai.
Kawo yanzu dai an tabbatar da gano gawarwaki takwas cikin 10, sai dai babu karin haske a kan wadanda aka gano din. Rahotanni farko da aka bayyana dai, na nuni da cewa baki dayan mutanen da ke cikin jirgin wanda ke kan hanyarsa ta zuwa St. Petersburg daga Moscow sun halaka a hadarin da ya afku a kauyen Kuzhenkin.
A watan Yunin wannan shekara ne dai, Prigozhin da sojojinsa na Wagner suka yi wani dan kwarya-kwaryan tawaye da ya nemi kwace iko da sansanonin sojojin kasar ta Rasha. Wannan matakin nasa ya sanya hukumomin kasar tilasta masa neman mafaka a makwabciyarsu Belarus, tare da bukatar dakarunsa da ko su bi shi ko kuma su shiga cikin rundunar sojojin kasar ta Rasha.