Babu sayar da makamai don yaki a Yemen
January 20, 2018Talla
Kakakin gwamnatin ta Jamus Steffen Seibert, ya ce majalisar tsaron kasa ce ta tabbatar da dakatar da ba da lasisin fitar da makaman, muddin bukatar ta saba wa tattaunawar zaman lafiya da ake yi. Wannan, wani sabon salo ne gwamnatin Jamus ke dauka na ganin an kai ga kafa sabuwar gwamnati ta la'akari da tattaunawar fahimtar juna da aka tsara. Tun a shekarar 2015 ne dai wasu kasashen Larabawa ke taron dangi kan mayakan tawayen Houthi, 'yan Shi'a a Yemen.
A bara ne kasar Saudiyya ta sanar da shirin sayen makaman Jamus, sai dai Jamus na jan kafa saboda matsin da take sha daga cikin gida kan batun kare 'yancin rayuwar jama'a.