1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban bankin Najeriya ya dauki mataki kan bankuna

January 11, 2024

Babban bankin Najeriya CBN ya rusa majalisar gudanarwar bankuna hudu da ake zargin tsohon gwamnansa ya saye ta hanyar amfani da kudade na haramun a lokacin da yake aiki.

https://p.dw.com/p/4b90r
NO FLASH Zentralbank von Nigeria
Hoto: public domain

Badakala ce da ke cike da sarkakiyar gaske, inda wani kwamiti da shugaban Najeriyar ya kafa ya rinka bankado zargin yadda aka rinka kwasar kudi daga asusun babban bankin kasar, ana fitar da su zuwa bankin Titan Trust, shi kuma ya sayi bankunan guda uku na Keystone da Polaris da kuma bankin Union inda suka zama mallakar tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele.

Wannan mataki da babban bankin ya dauka na rusa majalisun gudanarwar bankunan guda hudu, matakin farko ne na karbe kadarorin da ake zargin ya mallaka ta hanyoyi na haramun.

Tsabar kudi har dala miliyan 500 ne dai aka gano cewa an fitar da su daga bankin inda aka samar da bankin Titan Trust a badakalar da aka dade ba a ga irin ta ba a babban bankin Najeriyar da ya kamata ya zama mai tsawata wa sauran bankuna.

DW ta yi kokarin jin ta bakin babban bankin Najeriyar da ya ba da wannan umurni, amma jami'ar yada labaru a bankin ta ce ba za su ce uffan ba a yanzu, ganin cewa ana ci gaba da bincike da ma tuhumar tsohon gwamnan babban banki na Najeriya a kotu inda ya musanta aikata wani laifi a kan wannan batu.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin EmefieleHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Tun kafin kaiwa ga wannan lokaci dai shugaban kwamitin da aka kafa Jim Obaze ya ba da shawarar a maida bankunan mallakar gwamnatin Najeriya, domin an same su ne ta hanyar dukiya ta haram.

Daukan irin wadannan matakai dai na nuna alamu na sa ran samun ci gaba a yaki da cin da rashawa a Najeriyar, da ya saba wa abin da aka gani a gwamnatin da ta gabata.

Sai dai kuma ana ganin ba a saurin yabo a al'amarin da ke neman zamewa hallaya ta assha a kasar da cin hanci da rashawa ya zama babban kalubalen da ke jefa rayuwar jama'a cikin mawuyacin hali.