Atiku ya sallami APC mai mulki
November 24, 2017Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulkin kasar, Atiku Abubakar ya yi murabus daga jam'iyyar, abin da ke tabbatar da cewa zai kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben da za a yi kasa da shekaru biyu nan gaba. Atiku wanda ya yi matsayin mataimakin shugaban Najeriyar daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya ce APC ta Buhari, ta gaza samar da sauyin da ta yi ikirarin samarwa ga 'yan kasa.
Cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Juma'ar, tsohon mataimakin shugaban na Najeriya, ya jaddata rashin katabus din APC da suka kafa, musamman a bangaren matasa masu tasowa. Ana dai rade-raden Atiku Abubakar zai koma jam'iyyar PDP ne, inda ake ganin ta yiwu ya yi mata takara a babban zaben kasar na ranar 16 ga watan Fabrairun 2019.