An gano wasu bayanan sirri a gidan Biden
January 13, 2023Fadar White House ta Amirka, ta ce an gano wasu takardu da ke kunshe da bayanan sirrin gwamnati a gidan shugaban kasar Joe Biden da ke a Delaware.
Lauya na musamman ga Shugaba biden din Richard Sauber, ya tabbatar da samun wasu takardun da ya ce kanana ne a garejin mota da ma wani daki da ke kusa da Mr. Biden.
Shugaba Joe Biden ya ce yana bai wa ma'aikatar shari'ar kasar hadin kan da ya dace a kan wannan lamari.
A halin da ake ciki dai babban lauyan gwamnatin Amirkar Merrick Garland, ya nada wani lauyan da zai binciki irin rikon da shugaban ke yi wa irin wadannan takardu.
Gabanin zaben tsakiyar wa'adi da aka yi a Amirkar cikin watan Nuwambar bara ma an gano wasu irin wadannan takardu na bayanan sirri a gidan Shugaba Biden da ke a birnin Washington.
Idan ba a manta ba, shi ma tsohon shugaban Amirkar Donald Trump wanda Shugaba Biden ya gada na fuskantar bincike a kan lamarin da ya shafi takardun bayanan sirrin na gwamnati.