1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSweden

An bayyana zakarun Nobel na bana

October 2, 2023

Cibiyar da ke bayar da lambar yabo ta NOBEL ta sanar da Katalin Kariko da Drew Weissman a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel ta kiwon lafiya saboda gano rigakafin Corona.

https://p.dw.com/p/4X39Z
Wadanda suka ci kyautar Nobel na 2024
Wadanda suka ci kyautar Nobel na 2024Hoto: ANNA WEBBER/AFP

Kwararrun masu binciken su biyu sun nuna hazaka a daidai lokacin da duniya ke bukatar dauki na dakile annobar Corona da hakan ya gagari kundila tun farkon barkewar annobar. 

A watan Disambar 2020 ne Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da amfani da rigakafin na mRNA da hakan ya kubutar da miliyoyin mutane a duniya kamar yadda alkalan Nobel din suka bayyana.

 Kariko, 'yar shekara 68, da Weissman mai shekaru 64, da dukkan su ke aiki a jami'ar Pennsylvania da ke Amurka, sun kuma gudanar da ayyukan bincike da dama da ya ba su ikon samun lambobin karramawa da yawa.

Daga cikin ayyukan da Kariko ta gudanar har da batun cewa zamani ya wuce na amfani da kwayoyin halitta na gado DNA wajen binciken cututtuka, kasancewar wasu cututtukan ba gadon su ake yi ba, inda ta gabatar da binciken amfani da kimiyyar mRNA.