'Yar Belarus ta lashe kyautar Nobel ta 2022
October 7, 2022Shugabar kwamitin bayar da kyautar ta Nobel din Berit Reiss-Andersen ta siffanta kyautar ta bana da wani mataki na girmama kudurin kare hakkin dan Adam, dimukuradiyya da fahimtar zaman lafiya a kasashe uku masu makwabtaka wato Belarus da Rasha da Ukraine.
Baya ga kyautar zaman lafiya akwai kuma kyautar Adabi wace Anders Olsson ya jagoranci bayar da ita. Ya yi karin bayani kan dalilansu na bai wa Bafaranshiya Annie Ernaux kyautar Adabin ta Nobel.
"Rubutun Annie Ernaux yana karkashin tsari mai tafiya da lokaci. Kuma hakan ya bayyana a cikin shekara ta 2008, a cikin littafinta na Turanci, mai suna 'The Years" in ji Olsson
An dai samu martani daga shugabanni kan wannan kyautar zaman lafiya da aka bayar, inda shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta jinjina wa "bajinta da jajircewar" masu fafutukar kare hakkin dan Adam a Ukraine da Rasha da Belarus.
Gwamnatin Jamus ta wallafa cewa "Wadanda suka lashe kyautar sun yi adawa da adawa, kuma sun yi yunkuri na yaki da zalunci a cikin kungiyoyin fararen hula kamar musamman yadda rayuwa take a Rasha da Belarus."