1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta shirya da Koriya ta Arewa

April 9, 2018

Koriya ta Arewa da kasar Amirka za su magantu dangane da rigimar manyan makamai da ta kai kasashen biyu yin musayar zafafan kalamai. 

https://p.dw.com/p/2vjAd
Bildkombo Kim Jong Un und Donald Trump
Shugaba Kim Jong Un da Donald Trump na AmirkaHoto: Reuters/KCNA//Reuters/L. Jackson

Jami'ai a Koriya ta Arewa sun ce gwamnatin kasar ta magantu da Amirka dangane da yiwuwar tattaunawa kan rigimar nan ta manyan makamai da ta kai kasashen biyu yin musayar zafafan kalamai. Amincin dai ya sanya kwarin gwiwa, ga kama hanyar kai wa ga samun sulhu a tsakanin shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa Kim Jong Un.

A cikin watan jiya ne dai shugaba Trump ya amince da ganawa da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewar, abin kuma da zo wa kasashen duniya da matukar mamaki. 

A share guda kuma kasar China ce ta dakatar da fiton wasu kayayyaki da kuma fasahar manyan makamai zuwa Koriya ta Arewa, kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukata. Fasahohin dai sun hada da wadanda sojoji ke iya amfani da su, da ma na wasu fararen hula.