ECOWAS na son warware rikicin Nijar cikin sauki
September 21, 2023Talla
Idan za a iya tunawa dai, Kungiyar ECOWAS da Senegal ke da kujera a cikinta, ta yi barazanar daukar matakin soja domin mayar da Bazoum kan kujerarsa, kafin matsin lamba ya sa ta fifita hanyar tattaunawa.
Karin bayani: ECOWAS za ta dawo da dimukuradiyya a Nijar
A cikin wata hira da aka yi da shi a taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, Macky Salla ya ce shugaban ECOWAS kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubuna iya kokarinsa don samun mafita ta hanyoyin diflomasiyya, amma suna jiran sakamakon tattaunawa domin sanin alkiblar da suka fuskanta.