Allah ya yi wa Shimon Peres rasuwa
September 28, 2016Al'ummar Isra'ila da gwamnatin kasar da Firayim minista Benjamin Netanyahu za su ci gaba da tunawa da Shimon Peres dangane da irin jawaban da yake yi da kan dauki hankalin duniya...
"Ba tare da sasanta bangarorin biyu ba, ba za'a taba samun kasar Isra'ila da Falasdinu ba a daya hannu...Sai dai za'a ci gaba da samun kasasahe biyu a karkashin guda. Ya zamanto wajibi mu cimma matsaya, wanda zai nunar da cewar Isra'ila kasa ce mai zaman kanta ta yahudawa kuma ta dimokuradiyya"
Peres ya kasance daya daga cikin 'yan siyasa na Isra'ila na farko da suka amince da matsugunen Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Wannan ya zame masa tamkar lashe aman da ya yi na tsawon lokaci.
Wane ne Shimon Peres?
An haifi tsohon shugaban na Isr'aila Peres a shekarar 1923, a Wiszniewo da a da can yake kasar Poland. Lokacin da Jamusawa suka je wannan gari, sun tara Yahudawan a dakin bautarsu, tare da kulle dakin katakon kafin cunna musu wuta.
Sai dai duk da wannan kisan gilla da aka yiwa iyalin nasa, bayan yakin duniya na biyu, a siyasance Peres ya kasance cikin masu kokarin sasanta Jamus da Isra'ila. A shekara ta 1956, lokacin da ya cika shekara 33 kuma ya kasance babban darekta a ma'aikatar tsaro, ya zo neman agaji a wajen ministan tsaron Jamus Franz Joseph Strauß.
" Muna fuskantar barazana da hari daga ko wane bangare. Kuma dole Jamus ta dauki alhakin wani bangare na kare Isra'ila, kasancewarta karamar kasa kuma me rauni, saboda 'yan Nazi sun kashe kashi daya daga cikin uku na al'ummarta. "
Da farko wannan yarjejeniyar ta kasance cikin sirri. Shekaru 9 bayannan nan ne kasashen Jamus da Isra'ila suka mayar da dangantakarsu ta diplomasiyya. Perez ya kasa manta wannan lokaci....
" A lokacin ne na kara sanin Adenauer. Mutum ne mai wayo, ya na da fahimta, dangane da abin da ya zamanto wajibi ya aiwatar. Abin farin ciki shi ne, ya na da hulda ta kut-da-kut da Ben Gurion, wanda shi ma ke da ra'ayin cewar dole mu yi tanadin gina gaba, ba wai zamu kawai ci gaba da tuna baya ba".
Nasarori da rauni na Shimon Peres
Babbar nasarar da ya samu a tsawon rayuwarsa ita ce, lambar yabo ta Nobel da ya samu. A shekara ta 1994 Peresd a Firayim minista Rabin da shugaban Falasdinu Yasser Arafat suka samu lambar yabo kan fafutukarsu wajen warware rikicin yankin Gabas ta Tsakiya. Sama da shekaru 20 kenan aka cimma yarjejeniyar Oslo, amma har yanzu babu alamun warware rikicin.
" Yarjejeniyar Oslo ta sauya komai a yankin gabas ta tsakiya...babu gudu babu ja da baya".
A kasarsa dai wasu na yi masa kallon mutumin da ke amfani da damar da ya samu, marasa hangen nesa kan illolin abin da yake yi, wanda bai taba samun nasara ta hanyar zabe ba. Sai dai ko shakka babu, mutuwar Shimon Peres babban gibi ne a siyasar kasar Isra'ila da ma wakilinta a matakin kasa da kasa. Ya kan ce bai damu da abubuwan da suka shige dangane da aikinsa ba, ya kan yi hangen gaba ne kawai.