Magoya bayan Imran Khan sun ja daga a Pakistan
August 22, 2022Tun bayan tunbuke shi kan madafun iko ranar 10 ga watan Afrilu, tsohon Firaminista Imran Khan yake gangami a sassan kasar inda ake ganin yana zagon kasa ga gwamnatin Firaminista Shehbaz Sharif da kawancen jam'iyyun siyasar da ke mara masa baya.
Daruruwan magoyan bayan tsohon Firaminista Khan sun ja daga a unguwar masu hannu da shuni ta "Bani Gala", dab da harabar gidan Mr Khan sun kasa sun tsare, bisa hujjar cewa duk wani yunkuri na kama Imran Khan keta jan layi ne da suka shata.
'Yan gani kasheni na yi wa jami'an tsaron da ake hasashen kowane lokaci ka iya kutsawa gidan tsohon firaminista Khan don kama shi barazana, wasu daga ciki har da Muhammad Ayub, da ya yi takakkiya daga Lardin Peshawar na arewacin Pakistan don kare gwaninsa, na cewa "Za mu sadaukar da kanmu ta hanyar zanga-zanga da toshe duk hanyoyi, idan har gwamnati ta kama Imran Khan."
A wannan Lahadi 'yan sanda sun shigar da tuhumar yi wa 'yan sanda barazana da aikata ta'addanci kan tsohon tsohon Firaminista Khan, lamarin da ya kara zaman tankiya a siyasar kasar Pakistan. Akwai yiwuwar a daure tsohon firamnistan na tsawon shekaru, sai dai a wani mataki na kariya lauyoyinsa sun shigar da kara a gaban kotun koli a Islamabad, kuma kotun ta bayar da belinsa har zuwa wannan Alhamis.
Jam'iyyar Pakistan Tehreek-e-insaf (PTI) ta zargi ana yi wa jagoranta Imran Khan bita da kullin siyasa musamman ma zarge-zargen da ake yi masa da aikata laifi. "Muna Allah wadarai da yunkurin kamun siyasa da ake son yi wa Imran Khan, wanda hakan ka iya zama silar rikicin siyasa" In ji jam'iyyar PTI ta tshon firaminista Imran Khan.
An zabi Imran Khan a shekarar 2018 a matsayin sabon firaministan Pakistan, bisa tarin alkawuran yakar cin hanci da rashuwa, sai dai hakan ya faskara bayan da tattalin arzikin kasar ya fuskanci mummunan durkushewa.
Gwamnati ta hana kafafen yada labaran Pakistan wallafa duk wani jawabin Imran Khan, bisa hujjar cewa kalamunsa na hadasa kiyayya da tashin hankali tsakanin al'ummar Pakistan.