1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban Pakistan ya rusa majalisar dokoki

April 3, 2022

Matakin na nufin wajibi ne a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a cikin kwanaki 60, sabanin shekara mai zuwa da aka tsara gudanar da zaben tun da farko. Wannan ne kuma zai hana firaministan kasar cika wa'adinsa.

https://p.dw.com/p/49P4g
 Imran Khan
Hoto: Saiyna Bashir/REUTERS

Shugaban kasar Paksitan Dr. Arif Alvi, ya rusa majalisar dokokin kasar a wannan Lahadi. Matakin ya biyo bayan yunkurin tsige Firaminisatan kasar  Imran Khan ta hanyar kada masa kuri'ar yankan kauna da 'yan majalisar kasar suka yi. Mataimakin shugaban majalisar ta Pakistan ne dai ya dakatar da yunkurin, in da ya ce kudurin ya saba wa dokokin kasar.

Pakistan dai tana da tarihin rikicin shugabanci kala-kala. Tun daga shekara 1947, lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan Birtaniya, babu firaministan da ya taba yin cikakken wa'adin shekaru biyar ba tare da an yi masa juyin mulki ko kuma rikicin siyasa ya kawar da shi ba. A shekara ta 2018 ne dai Firaminista Khan mai ci ya hau mukamin.