Siyasar Jamhuriyar Nijar ta dauki sabon salo
An wallafa October 31, 2023sabuntawa ta karshe October 31, 2023A jamhuriyar Nijar watanni uku bayan juyin mulki da kuma jinginar da ayyukan jam'iyyun siyasa da hukumomin mulkin soja suka yi, wasu 'yan kasa sun zargin wasu 'yan siyasa da sauya sheka zuwa kungiyoyin farar hula inda suke neman yin tasiri a tafiyar mulkin rikon kwarya ta yadda za su yi sharar fage ga jam'iyyunsu kafin tafiya zabe. Sai dai a yayin da wasu ‘yan farar hular ke nisanta kansu da siyasa wasu na cewa ba laifi ba ne su yi siyasa da sunan farar hula.
Karin Bayani: EU ta kama hanyar kakaba wa Nijar takunkumin karya arziki
Tun dai washe garin juyin mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne bayan da hukumar mulkin soja ta CNSP ta sanar da dakatar da ayyukan jam'iyyun siyasar kasar, aka fara samu yaduwar kungiyoyin farar hula da suka fito suna da'awar kawo goyon bayan ga sojojin da suka yi juyin mulki.
Sannu a hankali ma wasu daga cikin wadannan ‘yan farar hula sun yi tasiri sosai ga hukumar mulkin rikon kwarya ta CNSP wacce ke aiki da shawarwarinsu wajen daukar matakai da dama. To sai dai wasu ‘yan kasar ta Nijar na ganin akasarin wadannan ‘yan farar hula ainahinsu ‘yan siyasa ne da ke fakewa a yanzu da inuwar farar hula domin ci gaba da ayyukansu ta yadda za su iya suma yin tasiri wajen shata manufofin mulkin rikon kwaryar ta yadda zai fi gyara jam'iyyarsu da share mata fagen lashe zabe a zabuka masu zuwa.
Sabon kawancen kungiyoyin farar hula na Dynamique Citoyenne na daga cikin kawancen kungiyoyin farar hula da ake zargi na rawa ne da bazar siyasar jam'iyyar PNDS Tarayya. To sai dai Malam Lawal Sallaou Tsayyabou na kawancen ya ce a demokradiyya ba lafi ba ne kungiyoyin farar hula su yi siyasa. Kungiyar Debout Citoyen da kuma Mouvement Patriotique pour la Souverainete wadanda ke sahun gaban goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki na daga cikin kungiyoyin da su kuma ake zargi da taka rawa ba bazar jam'iyyar lumana Afirka a cikin tafiyar mulkin rikon kwarya. To sai dai Malam Soumaila Muhamadou na kungiyar ta Debout Citoyen nisanta kansa ya yi da siyasa.
Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga rawar da rawar da wadannan kungiyoyin farar hula da wasu ke cewa masu zane ne za su ci gaba da takawa a mulkin rikon kwarya da kuma yadda makomarsu a lokacin da za a buga kogen siyasa a karshen mulkin rikon kwaryar.