1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bukatar gurfanar da Issoufou

Salissou Boukari LMJ
October 4, 2023

Kungiyar M62 da ke Jamhuriyar Nijar, ta shigar da karar tsohon shugaban kasar da take zargi da laifukan cin zarafin dan Adam da shigo da ta'addanci kasar da kuma daure mutane ba tare da bin dokoki na kasa da kasa ba.

https://p.dw.com/p/4X6vL
Nijar | Yamai | Mahamadou Issoufou
Karo na biyu ke nan da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ke fuskantar zargiHoto: AFP/I Sanogo

Kungiyar ta M26 ta kuma shigar da karar babban mai shigar da kara na gwamnati a gaban kotun  kasar da ke Yamaibabban birnin kasar. Cikin takardar shigar da karar da M62 ta mika ga ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa, ta gabatar da bukatar fara shari'ar adawa a kan  tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou da kuma duk wasu mutane da ayyukan binciken da za a gudanar za su shafa. Takardar ta M62 ta kara da cewa shigowar ayyukan ta'addanci a Nijar batu ne da aka yi da gangan wanda ya bai wa tsohon shugaban kasar cimma wasu bukatunsa ta re da shigo da sojojin kasashen waje da dama cikin kasar.

Jamhuriyar Nijar | Kotu | Kara | Mahamadou Issoufou
Kotun daukaka kara ta Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Sai dai wannan lamari ya soma samun suka daga wasu bangarori ya yin da wasu ke ganin cewa an dauki wannan matakin cikin fushi, wasu na ganin cewa kamar matsin kaimi ne ake yi wa hukumar mulkin soja ta CNSP domin ta dauki mataki maimakon a bar komai a hannun shari'a. A nasa bangaren shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin farar hula masu kare hakin dan Adam da kuma fadakarwa zuwa ga nuna kishin kasa mai albarka, Anda Garba Moussa sukar lamarin shigar da karar ya yi, inda ya ce an yi wa tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou butulci. Sai dai a fuskar masanin dokokin shari'a wani lauya kuma dan fafutuka na kungiyoyin farar hula Lirwana Abdourahamane na ganin lalle 'yacin su ne su shigar da wannan kara, amma kuma ya kamata a yi la'akari da matsayin Issoufou da ke na tsohon shugaban kasa wanda doka ta tsara yadda za a gurfanar da shi.