091210 Nobelboykott Oslo
December 9, 2010A lokacin bikin miƙa lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2010 da zai gudana a birnin Oslo a wannan Juma'ar, kujerar Liu Xiabao za ta kasance wayam, saboda Liu ɗin na ɗaure a wani kurkukun ƙasar China. A cikin mahalarta bikin ma ba za a ga wasu fuskokin ba, domin ƙasashe 20 sun bi sahun China wajen ƙauracewa bikin na bana.
Ƙasashe 65 ke da jakadu a Oslo babban birnin ƙasar Norway. A dangane da bikin ba da kyautar zaman lafiya ofisoshin jakadancin sun samu wasiƙu biyu-biyu. Ɗaya gayyata ce a hukumance daga kwamitin Nobel na Norway sannan ɗayar kuma daga ofishin jakadancin China dake buƙatar da su nesanta kansu daga bikin na bana. Geir Lundestad daraktan cibiyar Nobel ya yi karin bayani kamar haka.
"Mun tabbatar cewa a wannan shekara China ta yi ta kai gwauro tana kai mari domin ganin ƙasashe kaɗan ne za su amsa gayyatar mu. Yanzu za mu ga waɗanda za su ƙauracewa bikin saboda dalilai na siyasa ko wasu dalilai daban."
Ƙasa kamar Aljeriya ba ta amsa ba. Ko da yake ƙasashe 44 sun yi alƙawatin halartan wurin bikin amma ƙasashe 20 sun ce ba za su tura wakilansu zuwa shagulgulan na birnin Oslo ba. Ga da yawa a cikinsu akwai dalilai na tattalin arziki ko kuma suna goyon bayan adawar da gwamnatin Beijing ke nunawa manufofin kare haƙin bil Adama na ƙasashen yamma. Ƙasashe Larabawa shida na daga cikin ƙasashen da suka bi sahun Chinar kamar yadda Rainer Sollich shugaban sashen Larabci na DW ya tabbatar.
"Dukkansu ƙasashe ne da suke da matsaloli a ɓangaren kare haƙin ɗan Adam saboda haka ba su ga dalilin da zai sa su halarci bikin karrama wani da suka ɗauka ɗan adawa ne na gwamnatocinsu. Wani batun kuma shi ne na tattalin arziki domin China tana da angizo a wannan yanki, alal misali a Iraqi, Chinar ta fi kowace ƙasa zuba jari a ma'akatun man fetir da na iskar gas."
Su ma ƙasashen Ukraine da Rasha sun yi watsi da gayyatar ta kwamitin Nobel na birnin Oslo. Wani mai fafatukar kare haƙin ɗan Adam a Rasha Sergei Lukaschewski wanda kuma shi ne shugaban gidan tarihi na Andrei Sacharow a birnin Mosko ya yi ƙarin bayani.
"Rasha da China membobi ne a ƙungiyar haɗin kai ta Shanghai. Ɗaya daga cikin burinsu shi ne yaƙi da abin da suka kira wai tsattsauran ra'ayi, amma haƙiƙa abin nufi shi ne ƙasashen suna taimakawa junansu ne wajen yaƙi da ƙungiyoyin adawa na siyasa."
Sabiya wadda ita ta ƙauracewa bikin ko da yake ministan harkokin wajenta Vuk Jeremic ya ce ƙasarsa na daraja batun kare haƙin ɗan Adam amma ta fi ba da fifiko ga dangantaka tsakaninta da China. Wasu daga cikin ƙasashen da suka ƙarcewa bikin suna ƙarƙashin takunkuman ƙasashen yamma wato kamar Sudan da Iran da kuma Kuba.
Tun ba yau ba take-taken na China ya fito fili, inda a kwanakin bayan nan hukumomi a Beijing ke ƙara ɗaga murya wajen sukan lamirin kwamitin Nobel suna zarginsa da zama matattarar nuna ƙyamar China. A halin da ake ciki China ta ƙirƙiro kyautar ta ta zaman lafiya, inda a karon farko aka yi bikin miƙata a ranar Alhamis wato kwana guda gabanin bikin na birnin Oslo.
Mawallafa: Matthias von Hein/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu