1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen taron Ministocin kudi na G20

April 24, 2010

Ministocin kuɗi da shugabannin Bankunan ƙasa na G20 sun sanar da gano bakin zaren warware matsalar tattalin arzikin duniya.

https://p.dw.com/p/N5Ir
Taron Ministocin kuɗi da shugabannin bankunan tarayya na ƙasashen G-20 masu cigaban tattalin arzikiHoto: AP

Ministocin kuɗi da shugabannin bankunan tarayya na ƙasashe 20 masu cigaban tattalin arziki sun ce sun samo wata hanya managarciya wadda zata bunƙasa cigaban tattalin arzikin duniya fiye da yadda ake tsammani. Sai dai kuma suna taka tsantsan kada su kambama buri ganin matsalar bashi da ta dabaibaye ƙasar Girka wata alama ce dake nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da matsalar hada-hadar kuɗaɗe. Ministocin da shugabannin bankunan waɗanda suka kammala taron su jiya a birnin Washington DC sun kuma yi maraba da buƙatar Girka ta neman tallafi kuɗi daga Asusun bada lamuni na duniya da kuma ƙungiyar tarayyar Turai domin shawo kan matsalar da ta shiga.  A sanarwar bayan taron da suka gabatar Ministocin sun ƙi amincewa da batun sanya haraji akan bankuna. Haka kuma sun taɓo batun ko ya dace a bar ƙasar Sin ta cigaba da ɗaga darajar kuɗinta domin taƙaita bunƙasar kayayyakin da take fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Zainab Mohammed Abubakar