Ziyarar Steinmeier na Jamus da Ayrault na Faransa a Nijar
May 2, 2016
A yammacin ranar Litinin ne ministocin harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da na Jamus Frank-Walter Steinmeier ke fara wata ziyara a Jamhuriyar Nijar a wani rangadi a kasashen Afirka da ministocin suka kaddamar: Ministocin za su gana da hukumomi a Nijar kan batutuwa da dama da suka shafi tsaro musamman ma yaki da ta'addanci da batun bakin haure da Nijar ke zama kasar da matasan kasashen Afirka ke bi ta cikinta don zuwa Turai da kuma batutuwan raya kasa.
Ba tun yau ba ne dai kasashen na Faransa da Jamus ke tallafa wa Nijar ta fannoni daban-daban da suka hada da raya karkara da yaki da talauci da uwa uba matsalar da ta addabi kasar ta barazanar tsaro: Hasali ma daya daga cikin kasashen biyu na amfani da sansanin sojan kasar ta Nijar da filayen jiragenta a yaki da ta'addancin da take yi a kasashen yankin Sahel, a yayin da ita kuma kasar Jamus ke agaza wa Nijar wajan raya karkara da wasu huldodi masu tasiri sama da shekaru 50. Saboda haka ziyarar kusoshin diplomasiyar kasashen biyu na da matukar mahimmanci a cewar Alhaji Ibrahim Yacouba ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar:
"Na farko a karfafa huldar da ke tsakaninmu da yadda za mu cigaba da hulda inda za su taimaka mana wajen batutuwan da suka shafi noma da ruwa da tallafin karkara. Na uku shi ne batun da ya shafi duniya wato rashin kwanciyar hankali abin da ya shafi tsaro don kara inganta tsaro a kasarmu da duniya baki daya domin abin da yake faruwa idan ka kare kasarka to ka kare duniya baki daya."
Sai dai ga wasu 'yan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam irin su Alhaji Mustapha Kadi Oumani ziyarar ta ministocin kasashen biyu wata dama ce ga jamhuriyar Nijar da ta sheda wa duniya irin raunin da ta lura da akwai wajan cika alkawuran da tun da jimawa kasashen suka dauka musamman ma kan batun tsaro:
"Sun ce za su kawo ta su gudumuwa da kayan yaki don mu yaki ta'addanci amma ba su kawo ba sai muka ga cikas, saboda hakan yau muna farin ciki idan suka zo mu ce to ga abin da muke so domin idan kun bamu kayan aiki, mu muna da mazan yaki."
Ministocin biyu sun kuma kai ziyara kasar Mali da ita ma ke fama da matsalar rashin tsaro.