1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Ziyarar Kramp-Karrenbauer a Afirka

Mohammad Nasiru Awal
October 11, 2019

A wannan makon ziyarar aiki da ministar tsaron jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta kai wa sojojin Jamus da aka a kasashen Nijar da Mali ya dauki hankalin jaridun na Jamus

https://p.dw.com/p/3R8EA
Mali Besuch der Bundesverteidigungsministerin Annegret Kramp-Karrenbauer
Hoto: picture-alliance/dpa/A. I. Bänsch

Idan muka fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi a ranar Lahadi da ta gabata ministar tsaron ta fara ziyara, inda ta fara yada zango a Jamhuriyar Nijar kafin daga bisani ta karasa kasar Mali. Jaridar ta ce daga cikin sojojin Jamus fiye da 3300 da aka girke a ketare, kashi daya bisa uku ko dai yana aiki a Mali karkashin lemar tawagar sojojin EU ko ta Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA.

A lokacin ziyarar ministar ta ce sojojin Jamus za su dauki lokaci mai tsawo a kasar suna kuma bukatar tsare-tsaren da za su taimaka don tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Jaridar a farkon ziyarar, ministar ta yada zango ne birnin Yamai inda ta gana da shugabannin kasar sannan ta kai ziyara a sansanin jigilar kayayyaki ta jirgin sama na rundunar sojin Jamus zuwa kasar Mali.

Mali Besuch der Bundesverteidigungsministerin Annegret Kramp-Karrenbauer
Hoto: picture-alliance/dpa/A. I. Bänsch

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokacin kann ziyarar ta ministar tsaron Kramp-Karrenbauer a Nijar da Mali tana mai cewa shekaru shida bayan girke rundunar Minusma a Mali har yanzu ba ta canja zane ba dangane da matsalar rashin tsaro a kasar. Ta ce a yankin kan iyakoki da Burkina Faso da Nijar yanayin tsaro ma tabarbarewa ya yi a baya bayan nan. Saboda haka a cewar jaridar a sakarwa Mali ragamar tabbatar da tsaro ita kadai ba zabi ba ne, domin hakan ka iya dagula lamuran a ilahirin yankin Sahel, rikicin da ko ba dade ko ba jima zai iya bazuwa zuwa nahiyar Turai.

Taron neman sulhu da nufin kawo karshen rikici a kasar Kamaru da ya gudana a tsawon makon jiya ya dauki hankalin jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce shugaban kasa Paul Biya ya kira babban taron sasantawa na kasa to sai dai kasancewa tun da farko ya gindaya sharadin cewa ba za a tabo batun tsarin tarayya na fedaraliyya ko batun ballewa ba, ya sa masharhanta a Kamaru saka ayar tambaya game da manufar shirya taron.

Ganin cewa manyan jagororin ‘yan tawayen yankin masu magana da harshen Turancin Ingilishi sun kauracewa taron, ya tabbatar da hasashen da masana suka yi cewa taron ba zai haifar da wani abin a zo a gani ba. Sai dai a wani mataki na fatan alheri da zaman lafiya Shugaba Biya ya saki firsinoni 333, sannan a karshen mako aka yi wa dan adawa Maurice Kamto afuwa.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

A karshe sai jaridar Berliner Zeitung wadda ta ce wani katako na musamman daga kasar Ghana ka iya taka muhimmiyar rawa wajen sake gina majami'ar Notre Dame ta birnin Paris na kasar Faransa wadda gobara ta lalata a watan Afrilu. Jaridar ta ce majami'ar mai daddadden tarihi za ta iya samun gagarumar gudunmawar sake gina ta daga nahiyar Afirka.

Domin a kasar Faransa babu sauran katako mai kwari da za a iya amfani da shi na aikin sake gina majami'ar, amma kasar Ghana na da katakon na musamman saboda haka yanzu wani kamfani ya fara shirye-shiryen yadda za a samu kataon daga kasar ta Ghana.