1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Hillary Clinton a yankin Asia

Zainab MohammedFebruary 18, 2009

Ministar harkokin wajen Amurka ta isa birnin Jakarta

https://p.dw.com/p/Gwu0
Hillary Rodham ClintonHoto: AP

A rangadin aikinta na farko zuwa ƙasashen ketare, Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta isa ƙasar Indonesia. Wannan ziyarar dai bawai yana da nufin inganta dangantakar Amurkan da ƙasashen yankin kudancin Asia kaɗai ba, amma harda duniyar musulmi.

Ziyarar ta ministar harkokin wajen Amurkan zuwa Jakarta, fadar gwamnatin Indonesia dai nada nufin wanke Amurka a idanun duniyar musulmi. Duk dacewar Indonesia ta kasance ƙasar datafi kowace yawan al'ummar musulmi a duniya dai, tana taimakawa Amurkan wajen kampaign dinta na yaki da ayyukan tarzoma na ƙasa da ƙasa.

A dangane da hakane Clinton tace...."Kasancewar Indonesiya ce tafi yawan al'ummar musulmi a duniya,kuma ta ukun girma a Demokraɗiyya, zata taka muhimmiyyar rawa a makomar duniya nan gaba. Don haka ne muke fatan ingantuwan dangantaka a fannoni daban-daban da ita"

Hilary Clinton in Boston
Hillary Rodham ClintonHoto: AP

A baya dai Indonesiyan tasha sukan Amurkan dangane da yake yaken Iraki da Afganistan da tayi jagoranci ,tare da irin goyon da take nunawa Izraela a fili a dangane da rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Shugaba Barack Obama na Amurkan dai,ya sanar da manufofinsa na ketare, musamman dangane da dangantakar ƙasarsa da duniyar musulmi, wanda kuma ya fara yin tasiri a ƙasar ta Indonesia da wannan ziyara ta Hillary Clinton. Sai dai a cewar Micheal Green dake cibiyar nazarin harkokin tsaro na kasa da kasa dake Jakarta, kowace dangantaka ɓangarorin biyu zasu kulla zai danganta ne da halin da ake ciki a rikicin yankin gabas ta tsakiya....

"Dangantakar zata ta'allaka ne akan halin da ake ciki a rikicin yankin gabas ta tsakiya. Ba zamu iya nisantar da kammu daga Izraela, ta yadda zamu samu karɓuwa tsakanin al'ummar Indonesia ba. Don haka dangantakar zata samu rauni ,dangane da goyon bayan da muke bawa Izraela,da kuma halinda ake ciki a rikicin yankin gabas ta tsakiya"

BdT Muslimische Protestierende in Jakarta
Gangami ƙungiyoyin Musulmi a JakartaHoto: AP

A taron manema labaru na haɗin gwiwa da Hillary Clinton ta gudanar da takwaranta na indonesia Hassan Wirajuda,tace ɓangarorin biyu sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yankin dama Duniya baki ɗaya...

"Tace da farko dai mun tattauna manufofin shugabanninmu da fatan Kasashemmu na kafa ingantacciyyar tarayya,wanda zai taimaka wa cimma nasarar manufofimmu a wannan yankin da kuma Duniya baki ɗaya, waɗanda suka hadar da kare muhalli da sauyin yanayi zuwa harkokin kasuwanci da zuba jari ,ingantuwan Demokradiyya da Ilimi da tsaro, da kuma harkokin yaƙar ayyukan tarzoma na ƙasa da ƙasa"

Sama da jami'an tsaro dubu uku nedai aka girke a birenin na Jakarta domin tabbatar da tsaro. Tuni dai ƙungiyoyin musulmi da dama sukayi gangamin adawa da ziyarar ta ministan harkokin wajen Amurkan a Indonesia.