Share fagen ganawar Trump da Kim
May 30, 2018Talla
Ziyarar ta Kim Yong Chol wanda ke zama wani ja gaba a gwamnatin Koriya ta Arewan, na zaman ta share fagen tattaunawar da za a yi tsakanin shugaban Amirkan Donald Trump da kuma takwaransa na Koriyar ta Arewan Kim Jong Un. Kim Yong Chol dai zai gana da sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo a wata ziyara da ke zaman ta farko da wani babban jami'in Koriya ta Arewa ya kai Amirka tun tsahon shekaru 18 din da suka gabata. A ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa ne dai ake sa ran shugannin biyu za su yi wannan ganawa mai matukar tarihi a tsakaninsu.