Ziyarar Assad a Rasha
October 22, 2015Talla
Ana dai ci-gaba da yin tsokaci bisa ziyar ta ba zata da shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya kai kasar Rasha a jiya Laraba. Wanda shi ne karon farko da Assad ya fita kasar tun bayan shekaru biyar da fara yakin basasa a Damaskus. A ziyar Bashar Al-Assad ya gana da takwaransa Vladimir Putin inda suka tattauna rikicin Sirya da ma tallafin da Rasha ke bai wa gwamnatinsa. Amirka wanda ke marawa 'yan tawayen Siriya baya don kifar da gwamnatin Assad, ta soki irin tarbar girmamawa da karamcin da Rasha ta yi wa Assad yayin ziyarar.