1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugaban ƙasar Brazil a Britania

March 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5d

Shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inaccio Lula Dasylva, ya kai ziyara aiki a ƙasar Britania.

A tsawan yini 4, shugaban zai tantana da hukumomi Britania, a kan mahimman batutuwa, da su ka shafi hulɗoɗi tsakanin ƙasashen 2.

Wasu daga wannan batutuwa, sun jiɓanci ƙa´idoji cinikaya, na ƙasa da ƙasa, wanda a ke fuskantar taƙƙadama kan su a hukumar cinaki ta Majalisar Ɗinkin Dunia, wato WTO ko kuma OMC.

Sannan da maganar kwaskwarima, ga dokokin Majalisar Ɗinki Dunia, inda Barazil ke ɗaya daga ƙasashe masu takara samar kujera dindindin, a komotin sulhu.

A ɗaya wajen kuma, tawagogin ƙasashen2, za su tantana a kan batun yaƙi da talauci a dunia.

Saidai, babu daga cikin ajendar wannan ziyara, batun da ya a shafi mutuwar ɗan ƙasar Brazil ɗin nan, Jean Charles de menes, da jami´an tsaron Britania su ka harbe, a watan juli da ya gabata, bayan hare haren ta´adanci da su ka rutsa da wannan ƙasa.

Jaridar Daily Mail, ta ruwaito cewa, Sarauniyar Engla, ta roki gafara, da shugaban ƙasar Brazil, a ganawar da su ka yi yau.