1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Olesegun Obasanjo a ƙasar Amurika

March 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3g

Shugaban ƙasar Nigeria Olesegun Obasanjo, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Amurika, inda ya gana da takwaran sa Georges Bush.

Shugabanin 2, sun tantana, a kan batutuwa daban daban da su ka shafi harakokin diplomatia tsakanin Amurika da Nigeria.

Bush, yayi anfani da wannan dama, inda ya bayyana matuƙar gamsuwa, a game da capke tsofan shugaban ƙasar Liberia, Charles Taylor, da jami´an tsaro Nigeria su ka yi jiya, wanda kuma a halin yanzu, ke ƙasar Saleo, domin gurfana gaban kotun ƙasa da ƙasa, mai yanke hukunci manyan leffika.

Georges Bush, yace sun fara tunanin cenza kotun sharia´ar tsofan shugaban ,daga Saleo, zuwa kotun Majalisar Dinkin Dunia ta birnin Hage, kokuma la Haye.

Shugaba Obasanjo, ya ƙara jaddada cewar, tsofan shugaban Liberia, ya bukaci sulalewa, daga Nigeria inda ya sami mafaka, ba tare da haɗin kan hukumomin Nigeria ba, kamar yada jama´a da dama ke faɗi.

Bush da Obasanjo, sun kuma tantana a kan rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan,da halin da ake ciki a yankin Niger Delta.