1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya sa Zimbabwe ba ta samun tallafi?

Abdul-raheem Hassan
February 23, 2023

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar biyan bashin fiye da dala biliyan 6 da ake bin kasar daga kasashen ketere.

https://p.dw.com/p/4NuN9
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Dambudzo MnangagwaHoto: Dominika Zarzycka/NurPhoto/picture alliance

Mnangagwa ya ce tulin bashin sama da dala biliyan 14, ya hana kasar cin gajiyar samun lamuni na duniya da ake bukata sosai tun daga shekarar 2022.

"Basussuka da ake bin kasar Zimbabwe na ci gaba da zame mata karfen kafa sosai a fannin cigaba da gina kasa" in ji Shugaba Emmerson Mnangagwa.

Zimbabwe za ta biya manoma fararen fata diyyar dala biliyan uku da rabi na gonakinsu da gwamnatin tsohon Shugaban kasa Robert Mugabe ta kwata sama da shekaru 10 maimakon 20 da aka sanar shekaru uku da suka wuce.