1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Ukraine ta yi wa Jamus godiya

October 26, 2022

A yayin jawabin bidiyo da shugaban na Ukraine ke yi a kowanne dare, ya ce, an bai wa shugaban na Jamus tsaro ta sama a yayin da ake nuna masa irin barnar da gwamnatin Rasha ta yi a biranen Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Igdv
Ukraine, Kiew | Bundepräsident Steinmeier und Präsident Selenskyj
Hoto: Ukrainian Presidency/Handout/AApicture alliance

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gode wa shugaban kasar Jamus  Frank-Walter Steinmeier bisa ziyarar da ya kai kasar a ranar Talata. Zelensky ya isar da godiyarsa ga kasar Jamus kan taimakon da take ba su wajen kare kansu a yakin da Ukraine ke yi da Rasha.

To sai dai shugabannin biyu ba su ce 'uffan' ba a game da rashin fahimtar juna ta diflomasiyya da Zelenksy ya samu da Steinmeier, lamarin da ya hana shugaban kasar ta Jamus ziyartar Ukraine a watannin baya. To amma Steinmeier  ya jinjina wa Zelenksy a bisa jagorancin da yake yi wa Ukraine a cikin mawuyacin halin da kasarsa ta tsinci kanta na yaki da Rasha.