1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zartas da hukunci kan masu neman jinsi ɗaya a Bauchi

January 17, 2014

Wata kotun Musulunci da ke Bauchi, ta yanke wa wani matashi ɗan shekaru 20 da haihuwa hukuncin bulala bayan amsa laifin luwaɗi

https://p.dw.com/p/1AssJ
Symbolbild Homosexualität Schwules Paar
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata kotun sharia'ar Musulunci da ke Unguwar Tudun Alkali a cikin garin Bauchi, ta yanke wa wani matashi ɗan shekaru ashirin da haihuwa mai suna Mubarak Ibrahim hukuncin bulala ashirin wanda aka yi masa bayan yanke hukuncin nan take saboda amsa laifin cewa yayi luwadi da wani Principal ɗin makaranta. Alƙalin kotun Malam Nuhu Idris Muhammed yace matashin ya samu sassaucin hukuncin saboda ya furta cewar ya aikata wannan abin kyama shekaru bakwai da suka gabata inda ya ce wannan Principal shi yasa shi a wannan mummunar ɗabi'a amma kuma yana nadama da hakan kuma ya tuba ya daina.

Hukumar shari'ar musulunci ta jihar Bauchi ta ce ta bankaɗo wata ƙungiya da ta kunshi gungun masu yin luwaɗi a garin na Bauchi, bayan da wata jarida mai suna Leadership Hausa ta buga labarin cewar 'yan wannan ƙungiya sun yi taro a wani Hotel a garin na Bauchi tare da nufin jan hankalin sabbin wakilai. Hakan ya sanya hukumar ta dukufa wajen bincike, inda ta ce yanzu haka tana tsare da mutane 12, inda 11 daga cikinsu zasu fuskanci shari'ar musulunci, yayin da sauran mutum ɗaya, ɗan ƙabilar Igbo, wanda shi ma aka kama shi da laifin luwaɗin, za a yi masa shari'a da ba ta musulunci ba. Mallam Mustapha Baba Illela, shi ne shugabnan hukumar ta shari'ar musulunci. A jawabinsa ga DW yace:

"A watan da ya gabata a shekarar da ta gabata, mun ji cewar wasu yan luwaɗi sun kafa wata ƙungiya ta 'yan luwaɗi a jihar Bauchi. To mun kama bincike, kuma a binciken namu, Allah da ikonsa, ya zuwa yanzu dai mun sami nasarar kamawa da gurfanar da masu wannan aiki na luwaɗi bayan da su suka amsa laifukansu da bakinsu, wasu ma rubuta wa suka yi. Amma a haƙiƙa ita wannan ƙungiya da aka ce an kafa ta ɗin, ba mu iya cimma waɗannan da aka ce sune shuwagabannin ƙungiyar ba. Ba mamaki wasu sun canza sunayensu, wasu ma a hasashenmu ba 'yan jiha ba ne. Ya zuwa yanzu dai mun kama 12 waɗanda ake tsare da su, kuma an gabatar dasu gaban kotu domin a yanke masu hukunci."

A farkon wannan mako ne shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya raattaɓa hannu kan dokar da ta hana auren jinsi ɗaya, wadda ta tanadi hukuncin ɗauin shekaru 14 a gidan yari, to amma a dokar musulunci, hukuncin kisa ne kan wannan laifi ta hanyar jefewa. Akwai sauran mutane 11 da ake tuhuma, waɗanda suk kare kansu, ba tare da lauya a gaban kotun ba. Saboda ba'a sami lauya ko lauyoyi da suka fito domin kare su ba, saboda wasu matsaloli da ake fuskanta.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi: Ado Abdullahi Hazzad
Edita: Umaru Aliyu