1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin sanya siyasa a yaki da Boko Haram

Al-Amin Suleiman MuhammadMarch 25, 2015

Al'umma na zargin gwamnati da rashin daukar matakan da za su tabbatar da dorewar nasarorin da sojojin Najeriya suka yi a yankunan da aka 'yantar, wanda ta ke dangantawa da dalilai na siyasa.

https://p.dw.com/p/1ExXj
Abubakar Shekau
Hoto: picture alliance/AP Photo

Yayin da gwamnatin Najeriya ke yin shelar samun nasara a yakin da ta ke yi da kungiyar Boko Haram wanda shi ne ma zai ba da damar gudanar da zabukan kasa a karshen makon nan, 'yan kasar na bayyana cewa babu wani shiri da gwamnatin ta yi na dorewar wannan nasara, tana zargi yawancin ana alakantawa ne da siyasa.

Tuni dai rundunar sojojin Najeriya ta aiyyana cewa ta kawar da duk wata barazana ta Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna wanda aka fi sani da Boko Haram a jihohin Adamawa da Yobe a makonnin da suka gabata. A cewar babban hafsan tsaron Najeriya Laftanar Janar Kenneth Minimah sauran kananan hukumomi, da kauyuka kalilan ne suka saura a hannun 'yan Kungiyar inda kuma ya yi alwashin cewa ba za su kara sakewa wani bangare na kasar ya sake kubuta daga ikon kasar ba.

Nigeria Soldaten Archiv 2013
Sojin kasa da kasa na cigaba da yakar Boko Haram a da suka kame.Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Hanyoyin tabbatar da dorewar nasarorin

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan nasara da gwamnatin ke yin ikirarin samu a wannan yakin, wanda kawaye kuma makobtan ta ke taya ta da, domin kare yaduwar wannan rikici zuwa kasashen su kawai ba, har da ba da dama yin zabe da a baya aka dage saboda dalilai da aka bayar na tsaro. Sai dai yawancin al'ummar wannan yankin na alakanta wannan nasarar da neman jan hankalin masu jefa kuri'a a yankin, domin goyawa gwamnatin da ke kai baya don samun nasarar zaben.

Zargin da ake yiwa gwamnatin, na sanya siyasa a batun samun nasarar yaki ya kara fitowa fili bayan da shugaban Najeriya ya Goodluck Jonathan ya je yakin neman zabe jihar Yobe inda ya yi bayanin cewa ya kamata al'ummar yankin su zabe shi ko saboda nasarar da ya cimma cikin kankanin lokaci a yaki da Kungiyar Boko Haram.