1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin gwamnati da yada cin hanci a majalisar dokokin Najeriya

February 12, 2014

Jam'iyar APC mai adawa a Najeriya ta zargi PDP da ke mulki da yin amfani da kudin jama'a wajen sake neman karbuwa a majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/1B7hj
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A yayin da sannu a hankali fage na siyasar Tarayyar Najeriya ke daukar sabon launi dama fasali, jami'iyar APC ta adawa ta zargi 'yar uwarta ta PDP da kokari na bada toshi ta miliyoyi na daloli da nufin sake maido da 'yan tawayensu zuwa imani da gidan na wadata.

Sannu a hankali dai karatun yana kara girma. Sannu a hankali kuma yana wucewa da sanin Naira, a gwagwarmayar neman mallakin ruhin majalisun tarayyar kasar da yanzu haka aka fara karanta dalar Amirka a matsayin kudi na cin hanci don sauyin sheka.

Gwagwarmayar kuma da ta zauna ta kalli karuwar masu shiga da fita a cikin jam'iyar PDP mai mulki, jam'iyar kuma da yanzu haka ke fuskantar zargin amfani da dalar da nufin janye hankali don neman goyon baya.

Kama daga dalar Amirka miliyan daya ya zuwa miliyan biyu ne dai ke akwai a tsakanin duk wani dan jam'iyar APC da ya amince domin sauyin sheka ya zuwa PDP a tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa a fadar APC, da a sabon zagayen na sauyin sheka ta kai ga asarar rinjayenta amma kuma ke zargin PDP da sauya kalar cin hanci a cikin siyasa ta kasar.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Neman karbuwa ta hanyar cin hanci

Sanarwar APC da ta zauna ta kalli asarar wasu 'ya'yanta guda hudu a majalisar wakilan kasar a farkon wannan mako dai, ta ce abokiyar hammayar ta ta PDP ta ware dalar Amirka miliyan daya ga wakilai da miliyan biyu ga 'yan uwansu na dattawa sannan kuma da miliyan biyar ga 'ya'yan majalisar tarraya daga Rivers da ke kudu. Sannan kuma da dala miliyan 10 da ke zaman farashi mafi girma ga duk wani shugaba a majalisun biyu da ya amince shiga inuwar lemar domin taka rawa.

Zargin kuma da a fadar Honourable Bashir Babbale da ke zaman daya a cikin 'yan sauyin sheka daga PDP ya zuwa APC ke da alamu na kashin gaskiya a cikin sa.

“Ai abu ne da yake ba bako ba domin wanda ya dube ka yace za mu yi dadi da wuya domin ganin mun dawo daku, to ai dadin ba komai bane illa irin wannan dala miliyan dayan da ake magana ko kuma alkawari na mukami, ita kuma wahalar ita ce ayi amfani da jami'an tsaro ko hukumar EFCC ga masu laifi ko kuma ayi amfani da 'yan banga a ciwa wasu mutunci ba tare da jami'an tsaro sun yi magana ba. Kuma wannan ba sabon abu bane a zauren majalisa ma wadannan 'yan PDP da iyayen gidansu sun fadi kuma muna maganganu dasu cewar za su dawo da mu kuma wasu ma na dawowa.” .

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

PDP ta yi watsi da zargin yin amfani da kudi a majalisa

To sai dai koma wane irin tasiri ne dai sabuwar dabarar masu gidan na wadata ke iya dauka da nufin sake tattaro da watsatsen garken su dai, sannu a hankali dai suna samun nasara a yankin arewa maso yamma da ke zaman tungar 'yan tawayen da kuma sukai nasarar sake bankado da hankalin wasu 'yan majalisar biyu a Kano, biyu a jihar Zamfara sannan guda a jihar Sokoto domin shiga cikin inuwar lemar.

Nasarar kuma da a fadar Barrister Ibrahim Jalo da ke zaman mataimakin kakakin PDP na kasa ke da ruwa da tsaki da farga ta wuri ga sabbabin amaren PDP maimakon tunanin amfani da kudin da a cewarsa ke kama da mafarki:

“Ai yawancinsu daga Kano ne . Don irin siyasar da ake yau sun zama gwarzaye sun ga cewar lalle illalla abin da suka canka din na da wabi sun yi alwala da lam'a shi yasa suka ce a'a gara tun wuri mu yada mangoro mu huta da kuda. Ba maganar kudi sun dawo ne kan ra'ayi da kuma dubin abin da mazabunsu da mutanensu suka ga abin da zai kai ya kawo.”

Ya zuwa yanzu sana'ar sauyin shekar na sauyin salo da launi tare da komawa wata kafa ta warware bambancin ra'ayi na siyasa a matakai daban daban na siyasa ta jihohin kasar ta Najeriya.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh