1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin cin zarafin 'yan adawa a Nijar

Mahaman KantaFebruary 4, 2016

A yayin da aka shiga kusan mako daya da bude yakin neman zabe, shugabannin jam'iyyar Lumana Afrika ta Hama Amadu sun koka kan yadda hukumomi ke musu barazana.

https://p.dw.com/p/1Hq0r
Hoto: DW/M. Kanta

A halin yanzu dai baya ma ga shugaban jam'iyyar ta Moden Lumana Afirka Hama Amadou da ke tsare a gidan kaso duk kuwa da amince wa da takarar sa da kotun tsarin mulkin kasar ta yi, akwai kuma wasu shika-shikan jam'iyyar ta Hama Amadou da ake ci gaba da tsarewa a gidajan kaso tun kafin ma a kai ga lokacin yakin neman zabe da ke gudana a wannan lokaci, sai gashi kuma ana cikin yakin neman zaben kuma an kira wasu daga cikin shika-shikan jam'iyyar ta Lumana a gaban hukumar 'yan sanda bayan tarwatsa wani taron gangamin da suka shirya a ranar Talata da ta gabata bisa dalillan cewa sun tare hanyar da dantakara na jam'iyya mai mulki kuma shugaban kasa Issoufou Mahamadou zai wuce yayin da yake dawowa daga garin Fillingue inda ya je yakin neman zabe. Sai dai a cewar malam Aminou souley mataimakin sakataran yada labaran jam'iyyar ta Lumana ya yi tsokaci...

Niger Sympathisanten des früheren Parlamentspräsidenten Hama Amadou
Hoto: DW/D. Köpp

" Karfin iko ne kawai ake nuna mana alhali abun da doka ta ce idan an buda yakin neman zabe duk 'yan takara masu neman shugabancin kasa daya suke, domin yadda Issoufou Mahamadou yake fita ya yi yakin neman zaben sa, haka ta kamata shima Hama Amadou ya fita, ko Seini Oumarou ko Mahamane Ousmane da dai sauran su. Babu damar a hana wa wata jam'iyya gudanar da taron ta musamman ma a harabar cibiyarta, kenan yin haka wata fitane ce suka nema, domin shekaran jiya sun kira shugaban matasa na jam'iyyar ta Lumana Kimba Karimoun da Hamsou Garba mai yi wa jam'iyya waka, bayan an sallamosu sai kuma jiya aka sake kiranshi a ofishin 'yan sanda."

Kiraye-kirayen dai da jami'an tsaro na 'yan sanda ke yi wa 'yan jam'iyyar ta Moden Lumana Afrika na baya-bayannan ya hada da babban darectan yakin neman zaben jam'iyyar tsofon Minista Youba Diallo da kuma Hamsou Garba mawakiya wadda bayan an sallamota ta yi tsakaci kan kiran da aka yi mata...

" To ni dai ban san laifin da na yi ba, kuma laifin da ake so a ce na yi kilan ko ace na yi waka ko? To waka kuwa babu mai hana min waka domin sana'ata ce, kuma duk jam'iyyar da nake ra'ayi sai in yi mata waka. Ko su da suke wannan abun waka nawa na yi wa Mahamadou Issoufou, kuma ina ji da wakoki na ma suke yakin neman zabensu amma yanzu na zame mu su makiya har ana kai ni PJ wajan 'yan sanda. "

Niger Werbeschild für die Regierungspartei PNDS Tarayya
Hoto: DW/D. Köpp

Sai dai daga bangaren jam'iyya mai mulki ta bakin sakataran matasan jam'iyyar na birnin Yamai da kewaye Adamu Monzo ya yi na shi tsokaci kan wannan batu...

" Haba 'yan adawa sun yi ikon kasar nan shekara goma, mu ayyukan da muka yi na shekara biyar ya ninka nasu da suka yi na shekara goma sau biyar kenan mu bamu da fargaba da su domin jam'iyyunsu duk sun watse akwai abubuwan da suka aikata wanda hukuma take neman su domin ta yi musu tambayoyi kuma idan ba su da laifin komai za a sake su."

Tuni dai daga nasu bangare shugabannin kungiyoyin fararan hulla suka soma yin kashedi kan iri-irin abubuwan da ka iya mayar da hannun agogo baya, inda suka yi kira da a bi dokokin kasa don a zauna lafiya. A halin yanzu dai akasarin 'yan siyasan sun mayar da hankali ne ga yakin neman zabe a yankunan da ke kusan birnin Yamai kafin su fantsama ya zuwa sauran jihohin kasar.