1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
June 26, 2020

A Najeriya magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi ta IMN sun yi wata zanga-zangar lumana da nufin tilasta wa gwamnatin kasar sako Sheikh Ibrahim El-Zak zaky da mai dakinsa.

https://p.dw.com/p/3ePeQ
Nigeria Anhänger von Schiiten-Führer Ibrahim Zakzaky
Hoto: AFP/S. Adelakun

Magoya bayan kungiyar Islamic Movement of Nigeria IMN sun gudanar da wata zanga-zangar bukatar gwamnatin Najeriya hanzarta sakin jagoran kungiya Sheick Ibrahim Yakub  El- Zak zaky da mai dakinsa, wadanda ke daure a gidan kurkukun jihar Kaduna yau tsawon watanni.

Da yake magana da manema labarai kan dalilansu na fitowa zanga-zanagar, Kakakin kungiyar IMN Sheik Aliyu Umar Turmizy ya shedawa wakilinmu dalilansu na fitowa yin tattaklin a yau yana mai cewa suna bukatar ne ganin gwamnatin jihar Kaduna ta sako jagoransu ne biyo bayan wata kotu a Najeriya ta umarci yin haka tun daga farko.

Masu zanga-zangar dai sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta daukar matakan kare kashe-kashin al'umma a yankin Arewacin Najeriya.