1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar lumana domin fadakarwa game da yanayin da ake ciki a Dafur

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuBA

A ƙasashe da dama an gudanar da zanga zangar lumana a ranar Lahadi domin jawo hankalin shugabanin duniya da kuma Majalisar ɗinkin duniya su ƙara azama wajen kawo ƙarshen rikicin Dafur. A birnin Rome masu zanga zangar sun sanya fararen riguna da aka yiwa feshin jini inda suka yi tattaki zuwa tsakiyar birnin suna masu kira kawo ƙarshen wahalhalun da dubban yan gudun hijirar Dafur waɗanda ke zaune a sansanoni daban daban suke ciki. Zanga zangar ta gudana a ƙasashe fiye da 30 waɗanda suka haɗa da Australia da Masar da Jamus da japan da Mongolia da Nigeria da Afrika ta kudu da kuma ƙasar Amurka. A birnin London kuwa masu zanga zangar sun yi maci ne tun daga Ofshin jakadancin Sudan izuwa fadar P/M Britaniya Gordon Brown a Downing Street ɗauke da ƙyallye da aka rubuta dakatar da kisan kiyashi a Dafur da Fyaɗe da kuma azabtarwa. Da yake jawabi sabon Minista mai kula da alámuran Afrika Malloch Brown yace alámura sun taɓarɓare a Dafur fiye da yadda ake tsammani, yana mai cewa babu wata maslaha ta siyasa da zata warware wannan rikici.