1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar goyon bayan gwamnati a Nijar

Salissou Boukari
March 4, 2018

Dubban mutane ne suka fito a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, domin nuna goyon baya ga Shugaba Issoufou Mahamadou da kuma dokar kasafin kudin ta 2018 da kungiyoyin fararan hula ke nuna adawa da ita.

https://p.dw.com/p/2tfP7
Protest gegen Boko Haram in Niamey, Niger
Hoto: AFP/Getty Images/B. Hama

Wannan zanga-zanga ta masu mulki a Jamhuriyar ta Nijar, na zuwa ne a lokacin da kungiyoyin fararan hula da 'yan adawa ke ci gaba da nuna adawa da wannan doka ta kasafin kudi ta 2018 da suka ce ta haddasa tsadar rayuwa a kasar. Gamayyar jam'iyyun da ke mulki ne dai suka kira wannan zanga-zanga ta nuna goyon baya, ciki har da ministoci, da 'yan majalisar dokoki da sauran magoya baya.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi ta rera wakoki na yabon Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu ke dauke da hotunansa inda aka rubuta "Shugaba mai samar da zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa". A gaban dubban jama'ar da suka halarci taron gangamin, ministan cikin gida Bazoum Mohamed wanda kuma shi ne shugaban jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, ya zargi 'yan jam'iyyar adawa ta MODEN FA Lumana ta Hama Amadou tsohon firaminista kana tsohon shugaban majalisar dokoki da saka rigunan kungiyoyin fararan hula domin cimma wani buri ta hanyar amfani da dokar kasafin kudin kasar ta 2018.