1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaro daya ya mutu a zanga-zanga a Guinea

Gazali Abdou Tasawa
October 14, 2019

A kasar Guinea Conakry hukumomin kiwon lafiya a birnin Conakry sun ce akalla yaro daya ya rasu wasu biyu sun ji rauni a sakamakon harbin bindiga a lokacin zanga-zangar adawa da yinkurin tazarcen Shugaba Alpha Conde.

https://p.dw.com/p/3RH5h
Guinea Conakry | Proteste & Ausschreitungen
Hoto: Getty Images/AFP/C. Binani

A kasar Guinea Konakry hukumomin kiwon lafiya a birnin Conakry sun ce akalla yara daya ya rasu wasu biyu sun ji rauni a sakamakon harbin bindiga a lokacin dauki ba dadin da aka yini ana yi a ranar Litinin tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma dubban masu zanga-zangar da suka fantsama a unguwanni da dama na birnin domin nuna adawa da yinkurin tazarcen Shugaba Alpha Conde da ke son yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin sake tsayawa takara a karo na uku a zaben 2020.

 Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa masu zanga-zangar wadanda suka bazu musamman a unguwannin kewayen birnin na Conakry sun datse hanyoyi tare da kona tayu kana suka yi ta ruwan duwarwatsu kan jami'an kwatar da tarzoma wanda suka yi ta mayar da martani ta hanyar harba hayaki mai sa kwalla da ma buda masu wuta da bindiga. 

Birnin na Konakry dai ya kasance kwangalam a wannan rana bayan da shaguna da kasuwanni suka kasance a rufe a yayin da jami'an tsaro suka ja daga a gaban fadar shugaban kasa da ma'aikatun gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen ketare a birnin.