Zanga-zangar adawa da kyamar 'yan Habasha a Isra'ila
May 4, 2015'Yan sanda a babban birnin kasuwancin Isra'ila Tel Aviv, sun tarwatsa wani gangami na 'yan kasar masu tsatson kasar Habasha da suka shirya zanga-zangar adawa da nuna musu wariya da ma cin zarafi da jami'an 'yan sanda ke musu.
Wasu sun yi amfani da duwatsu da kwalabe wajen jifan 'yan sandan, inda suma suka mai da martani ta hanyar amfani da fesa musu ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye.
An dai cafke wasu da ga cikin masu zanga-zangar inda wasu kuma da suka hadar da 'yan sanda suka sami raunuka.
Tuni dai firaministan kasar ta Isra'ila Benjamin Netanjahu ya yi kira da a kwantar da hankula, sannan ya bukaci zaman tattaunawa da masu fafutikar 'yan asalin kasar Habasha a yau Litinin.
Zanga-zangar da ta fara ranar Lahadi dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan fitar wani faifain bidiyo da ya nuna wasu 'yan sandan Isra'ila biyu sun farwa wani sojan Isra'ila dan asalin kasar ta Habasha.