1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Yemen

March 20, 2011

Jakadan Yemen a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi murabus sakamakon tashe-tashen hankula a Yemen

https://p.dw.com/p/10czZ
Masu zanga-zanga a YemenHoto: dapd

Abdallah Alsaidi, jakadan Yemen a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi murabus sakamakon gumurzun da jami'an tsaro a Yeman suke yi da masu zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati a ƙasar.

Jami'ai a hukumar da ke kula da harkokin wajen Yemen sun ce Mr Alsaidi ya aika da takardan yin murabus ɗin na sa ne zuwa ofishin shugaban ƙasar da ranar yau.

Wannan murabus ya zo ne bayan da wasu manyan shugabanin jamiyyar da ke ci guda biyu, suma suka miƙa na su takardun yin murabus ɗin domin nuna adawar su da kisan masu zanga-zangar da aka yi a ranar juma'ar da ta gabata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Usman Shehu Usman